Majalisa Ta Kalubalanci Soji Su Kubutar Da Mata 300 Da Boko Haram Ta Sace

IMG 20240308 WA0095

‘Yan majalisar wakilai sun bu?aci hukumomin tsaro da su kubutar da mata kimanin 300 da aka yi garkuwa da su a jihar Borno a makon jiya. An bayyana cewa wasu da ake zargin maya?an Boko Haram ne suka yi garkuwa da matan a lokacin da suke neman itace a dajin Gamborou Ngala.

Da take gabatar da ?udiri kan lamarin a zauren majalisar a ranar Alhamis, ?ar majalisa mai wakiltar mazabar Bama/Ngala/Kalabalge ta jihar Borno, Zainab Gimba, ta bayyana sace ?an matan a matsayin abin damuwa.

?an majalisa sun damu da sace mata a Borno Ta ce sace matan abun sosa zuciya ne kamar yadda aka sace ?an matan sakandiren gwamnati da ke Chibok a watan Afrilun 2014, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.

A kalamanta: “Ina so in sanar da majalisar cewa an sace mata kimanin 300 a lokacin da suke nemo itacen amfani a gida da sayarwa a maza?a ta. “Ina kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ganin an ceto wa?annan matan da suka je neman abincinsu na yau da kullum.

Majalisar ta lura cewa wannan shi ne sace-sace mafi girma karo na biyu bayan sace ?an matan Chibok da aka yi a shekarar 2014 duk da cewa, har yanzu wasu daga cikin wa?annan ?an matan na hannunsu.”

A nasa jawabin mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ?ara kaimi wajen ceto matan da aka sace. Bayan da majalisar ta amince da ?udurin, an mi?a shi ga kwamitin tsaro da hukumar bada agajin gaggawa ta ?asa.

Related posts

Leave a Comment