Kudirin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin Nijeriya da zai takaita kwanakin gudanar da shari’a a kasar, ya tsallake zuwa karatu na biyu a majalisar wakilai.
Kudirin wanda Luke Onofiok ya gabatar, na neman a yi gyara ga sashe na 287 na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 domin takaice kwanakin da za a dauka don gama ko wace irin shari’a a kasar.
Onofiok ya ce wanda ya ce kayyade kwana 200 a matsayin lokacin yanke hukuncin ko wace shari’a, ya ce hakan zai taimaka wajen rage cinkoso a gidajen yari, saidai ya ce kudirin ba zai shafi shari’un zabe ba.
Da yake goyon bayan kudirin mai tsawatarwa na majalisar Muhammad Monguno, ya yi bayanin cewa kudirin dokar ya sha banban da dokar laifuka da aiwatar da shari’a.
Saidai kuma, da yake nuna rashin amincewarsa da kudirin Uzoma Abonta ya shawarci majalisar ta watsar da kudirin yana mai cewa takaita lokacin shari’ar zai iya zama hanyar da masu laifi za su iya guje wa hukunci, maimakon tabbatar da hukuncin.
A nasa jawabin kakakin majalisar Femi Gbajabiamila, ya ce za a warware duk wata badakala idan zancen ya je gaban kwamiti.
