?an Majalisar Wakilai a tarayyar Najeriya Kingsley Chinda, ya ce akwai maganar shirye-shiryen fara tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a zauren majalisa.
Dan majalisar ya bayyana cewa shi da wasu ‘Yan majalisa sun fara wayar da kan abokansu domin su amince a tsige Buhari, saboda gazawar Shugaban ta fuskoki da dama musanman fannin tsaro.
Chinda ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a wani gidan Radion FM da ke kan mita 92.3 a Fatakwal, jihar Ribas.
Kazalika, ya mayar da martani a kan kiran da ginshikin majalisa, Alhassan Ado Doguwa, ya yi na neman a hukunta shi saboda kiran a tsige Buhari.
“Muna tattauna wa da abokanmu kuma muna tuntubar ‘yan Nijeriya kuma muna karfafawa ‘yan kasa gwuiwar su yi magana da mambobin da ke wakitarsu. Idan jama’ar mazabar Doguwa suka ce masa muna son ka saka hannu a kan takardar tsige shugaban kasa, bashi da wani iko na kin goya musu baya,” a cewarsa.
Honarabul Chinda ya zargi shugaba Buhari da gaza sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya rataya masa na tabbatar da tsaro a Nijeriya.
A wani labarin na tsohon shugaban majalisar dattijai, Anyim Pius Anyim, ya ce sai mutanen yankin kudu maso gabashin kasar nan, na ‘yan kabilar Igbo, sun sauya halayyarsu kafin su samu takarar kujerar shugaban kasa.
Sanata Anyim, ya yi wannan i?irari ne a wani biki mai taken World Igbo Summit, wanda jami’ar Gregory dake Uturu a jihar Abia ta shirya a karo na shida, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Cikin bayaninsa mai taken, “Duban tsanaki kan bu?atar ?abilar Igbo ga mulkin ?asar nan tare da tsarin cimma hakan,” Anyim ya nuna gi?in dake akwai na ?allewa ko sauya tsarin fasalin ?asar nan.
