Lokaci Ya Yi Na Daukar Matasa 774,000 Aikin Yakar ‘Yan Bindiga – El Rufa’i

Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai na Jihar Kaduna ya shawarci gwamnatin Najeriya ta ?auki matasa 1,000 daga kowace ?aramar hukuma aikin bayar da tsaro don ya?ar ‘yan fashin daji masu garkuwa da mutane.

Da yake magana jim ka?an bayan mi?a masa rahoto kan matsalar tsaro a jihar ranar Laraba, El-Rufai ya ce babu wata hanyar ya?i da ‘yan fashin daji illa “yi musu ruwan wuta a lokaci guda”, abin da ya sa yake son a ?auki matasa 774,000 aikin.

“Ina kira ga jihohi 36 da su ?ullo da wani shirin gaggawa na ?aukar mutane aiki a rundunonin tsaro. Gwamnati ka iya sauya halin da ake ciki idan ta ?auki matasa 1,000 aiki daga kowace ?aramar hukuma a fa?in ?asa.

“Hakan zai zama gagarumin adadi na dakaru a fagen daga tun bayan ya?in basasa. Adadin sabbin dakaru 774,000 a filin ya?i zai kasance babbar hanyar gamawa da miyagu da kuma samar da aikin yi.”

Kazalika, gwamnan ya nemi gwamnatin Shugaba Buhari ta ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda “saboda sojoji su samu damar kashe su ba tare da wata matsala ba”, in ji shi.

“Mu a Kaduna mun sha neman a ayyana ‘yan fashin nan a matsayin ‘yan ta’adda. Mun rubuta wasi?u ga gwamnatin tarayya tun 2017 muna neman a yi hakan saboda ayyana su ne ka?ai zai bai wa sojoji damar karkashe wa?annan ‘yan fashin ba tare da wani abu ya biyo baya ba daga ?asashen duniya.”

Sabon rahoton da aka gabatar wa El-Rufai a yau ya nuna cewa mutum 343 aka kashe a Kaduna daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021 sakamakon ayyukan ‘yan fashi da kuma rikicin ?abilanci a jihar.

Haka nan, ‘yan fashin dajin sun sace mutum 830 cikin wata ukun da rahoton ya bayar da bayanai a kai tare da raunata 210.

Related posts

Leave a Comment