Lokaci Ya Yi Da Yakamata A Damka Ragamar Najeriya A Hannun Mata – Gwamnan APC

Rahotanni dake shigo mana daga Akure babban birnin Jihar Ondo na bayyana cewar Gwamnan jihar Rotimi Akeredolu, yace mata suna da kwarewar da zasu ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta idan aka basu dama.

An ruwaito cewa Gwamnan na ganin tun da maza sun gaza gyara Najeriya, wannan lokacin ne da ya dace mata su shugabanci kasar nan domin su gwada irin tasu basirar.

Gwamna Akeredolu ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabin bu?e babban taron mata (NWC), karo na 21, wanda ?ungiyar matan Legas (COWLSO) ta shirya.

Rahoto ya nuna cewa an yi wa babban taron matan na tsawon kwanaki uku taken “Mata mu farka Domin Fuskantar Kalubalen dake gaba”.

A jawabin gwamnan yace: “Bai kamata a watsar da mata ba matukar ana son cigaban Najeriya. Abinda ya dace shine ko dai a ?auko su a basu mu?amai ko kuma a basu ragamar mulkin baki ?aya.” “Maza sun kasa tafiyar da ?asar nan yadda ya kamata, mazan sun gaza, ina ganin abubuwa zasu fi gyaruwa idan aka jawo mata.”

“Ya kamata mata su wuce matakin rawa da wa?a a wurin taron ya?in neman za?e na siyasa, ya dace su yi wani abu na daban.”

A cewar gwamna Akeredolu, ya kamata a maida hankali wurin horas da ?aya mata su san rawar da zasu iya takawa nan gaba domin gobensu. “Tarihin Najeriya cike yake da ?wazon mata saboda haka ya zama wajibi mu rinka yaba musu.”

Babu wata al’umma da zata maida mata koma baya kuma ta yi tsammanin samun cigaba. Idan ana son Najeriya ta cigaba to ya zama wajibi mata su karbi ragamar ?asar nan. “Ni a shirye nake na zauna karkashin mulkin mata, ya kamata kowa ya shirya, domin mata sun iya jagoranci.”

Related posts

Leave a Comment