?ungiyar likitoci ?asar nan sun yi barazanar zasu tsunduma yajin aiki matu?ar gwamnatin ?asar nan bata biya musu bu?atunsu ba.
?ungiyar tace zata saurari gwamnati daga nan zuwa ?aya ga watan
Afrilu idan ba’a biya musu bu?atun su ba zasu shiga yajin aiki, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
A wata sanarwa da ?ungiyar ta fitar bayan babban taron ta na ?asa, ?ungiyar ta bayyana cewa bu?atun nata sun ha?a da biyan likitoci albashin su da aka ri?e.Da kuma biyan albashin watan Maris da muke ciki kafin 31 ga watan Maris ?in.
Sauran bu?atun sun ha?a da: biyan mambobin ?ungiyar hakko?in su da suke bin bashi harda na watan Maris musamman na jihohi da kuma ma’aikatan lafiya na makarantun gaba da sakandire.
Da kuma biyansu ku?a?en su na aikin ha?ari da suke yi, 50% na asalin albashin ma’aikatan lafiya da kuma ku?a?en su na COVID19 musamman a jihohin ?asar nan.
?ungiyar likitocin na cikin gida NARD ta kuma yi kira da a canza shugaban likitoci na (MDCN) saboda gazawar sa wajen gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
Hakan zai bada cikakkiyar damar aiwatar da gyaran tsarin likitocin cikin gida ba tare da wani tsaiko ba.
NARD ta kuma kara yin kira da biyan ragowar albashinsu na shekarun 2014, 2015 da kuma 2016 ga mambobinta dake makarantun gaba da sakandire, na jihohi, kamar yadda a kayi yarjejeniya da su a baya.
Hakanan kuma ?ungiyar ta yi kira da a biya ku?a?en inshora na ma’aikatan da suka rasa rayukansu a bakin aiki musamman wa?anda suka rasu saboda kamuwa da cutar korona.
Sannan kuma likitocin na bu?atar a gaggauta biyan ku?a?en bada horo na shekarar 2020 da 2021 ga mambobinta harda wa?anda ke aiki ?ar?ashin gwamnatocin jihohi.
