Legas: Hukumar EFCC Ta Yi Nasarar Damke Janar Na Bogi

Labarin dake shigo mana daga Birnin Ikko na jihar Legas na bayyana cewar Hukumar EFCC ta kama wani sojan bogi mai mu?amin Manjo Janar inda aka kama shi bisa zargin zamba ta naira miliyan 270.

Hukumar ta EFCC ta kama Bolarinwa Oluwasegun wanda ya yi i?irarin cewa Shugaba Buhari ya za?e shi a matsayin shugaban sojojin ?asa na Najeriyar.

Mista Bolarinwa ya ro?i wani kamfani na Kodef Clearing Resources da ya ba shi ku?i domin a tabbatar da shi a matsayin shugaban.

Haka kuma ana zarginsa da yin wata takarda ta bogi da sa hannun shugaban Najeriya wadda ke nuna i?irarin da ya yi na za?ar shi domin shawo kan kamfanin ya ba shi ku?in.

Related posts

Leave a Comment