Kungiyar gidajen ya?a labarai Talabijin da Rediyo masu zaman kansu na ?asa, ta koka dangane da halin da matsalar tsaro ke cigaba da addabar ?asa musamman yankin Arewacin Najeriya.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da ta fitar ranar Asabar wacce take ?auke da sanya hannun Shugaban kungiyar na ?asa Guy Murray Bruce da mataimakin shi Alhaji Tijjani Ramalan kuma aka rarraba ta ga manema labarai.
Kungiyar ta bayyana cewar halin da tsaro ke ciki yanzu a Najeriya tabbas abin tsoro da fargaba ne akan makomar kasar, domin lamari ne da ya faro a wani yanki guda sai gashi a yanzu ya mamaye ?asar gaba ?aya.
“Mun wayi gari ayyukan ta’addanci sun mamaye kasar, fashi da makami yin garkuwa da mutane rikicin manoma da makiyaya, babu wata kasa a duniya da za ta iya wanzuwa muddin tana fuskantar wadannan manyan kalubale”.
“Babu shakka fuskantar wadannan matsaloli na bukatar gudummuwar dukkanin bangarorin kasa baki daya, da kungiyoyin addini da yankuna, amma ya zamana wasu da ba sa fatan ganin ?orewar kasar na cigaba da rura wuta fitina domin kawo cikas a ciki.
Kungiyar ta bayyana cewar tana da kyakkyawan imani da yakini akan cewa da akwai hikima ta Allah Ubangiji da ya ha?a mu wuri guda cikin ?asa ?aya mai mabanbanta al’umma, bisa ga haka muna kira da babbar murya ga dukkanin jama’ar Najeriya da su rungumi juna da tattalin zaman lafiya.
Kungiyar ta bayyana cewar a halin yanzu duniya na cikin wani yanayi na cigaba akan harkar ya?a labarai, kuma a matsayin ?ungiya ta kafafen yada labarai masu zaman kansu suna yin dukkanin kokari da ha?a kai da Gwamnati wajen wayar da kan al’umma muhimmanci na zaman lafiya da zaman tare.
Kungiyar ta kuma bayyana cewar za ta gabatar da bukatar ?aukar nauyi na lokaci na kimanin rabin Biliyan wato naira Milyan 500 ga kwamitin Shugaban ?asa mai ya?i da cutar CORONA a gangamin ya?i da cutar da za’a yi nan gaba a gidajen ya?a labarai Talabijin da Rediyo a fadin kasar.
Daga karshe ?ungiyar sun yaba da ?o?arin da jami’an tsaron kasar ke yi dare da rana na ya?i da ta’addanci, inda suka yi musu kyakkyawar fata da addu’ar samun nasara a muhimmin aikin da ke gabansu.
