Kotun Koli Ta Yi Fatali Da Dokar Da Buhari Ya Sanya Wa Hannu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Kotun ?oli ta yi watsi da doka mai lamba goma wadda aka fi sani da “Presidential Executive Order No. 00-10 of 2020” wadda ta bayar da umarni ga babban akanta janar ya cire ku?a?e kai tsaye daga alawus-alawus na jihohi domin bai wa ?angarorin shari’a.

Al?alan Kotun ?olin duka wa?anda suka yi zama a ranar Juma’a sun amince da cewa dokar da shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi ta sa?a ?a’idar kundin tsarin mulki.

A bara ne babban lauyan gwamnatin tarayya ya shigar da ?ara a gaban Kotun ?olin domin ?alubalantar halarcin dokar mai lamba goma wadda gwamnati ta yi a bara domin ta sakar wa ?angarorin shari’a da ma’aikatan majalisu na jihohi mara su samu ku?insu kai tsaye daga tarayya.

Al?alan kotun sun ce dokar mai lamba goma a bayyana take cewa ta sa?a doka ta hanyar cin karo da sashe na shida da takwas uku cikin baka na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wanda ya bai wa gwamnatin tarayyya damar bai wa kotunan jihohi da na shari’a da na ?aukaka ?ara da na gargajiya ku?i.

Haka kuma al?alan Kotun ?olin shida sun amince da hukuncin sauran al?alan inda suka ce da gaske gwamnatin ?asar ba ta da ikon bayar da irin wannan doka.

Haka kuma jihohi sun kai kuka ga al?alan kotun inda suka ce suna amfani da ku?a?en su wajen gudanar da manyan ayyukan kotun tun daga 2009 inda suke so gwamnatin tarayya ta mayar musu da ku?insu.

Kan wannan batu, al?alan Kotun ?olin hu?u sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta biya ko sisi ba haka kuma gwamnatin jihohin za su ci gaba da bayar da ku?a?e ga kotunan da ke jihohin.

Idan ba a manta ba Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya saka hannu a doka mai lamba goma a ranar 22 ga watan Mayun 2021 domin sakar wa ?angaren shari’a da majalisu na jihohin Najeriya 36 mara su samu ku?a?e.

Dokar na nufin babban akanta janar na Najeriya na da damar cire ku?in jihohi domin bai wa majalisu da kuma ?angarorin shari’a na jihohi.

A lokacin da shugaban ya sanar da saka hannu kan dokar a shafin Twitter a lokacin, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin iya bakin ?o?arinta domin ?ara inganta ayyukan gwamnatin a ?asar.

Shugaban ya bayyana cewa ya yi dokar ne bisa ?arfin da sashe na biyar na kundin tsarin mulki na 1999 ya bashi.

Wannan na nufin ku?in da gwamnatin tarayya ke bai wa ?angarorin shari’a na jihohi da majalisu ba zai ci gaba da kasancewa a hannun gwamnoni ba.

Hakan ne ya sa jihohi 36 na Najeriya suka fusata har manyan lauyoyinsu suka shigar da ?ara a ranar 17 ga watan Satumban 2020 domin ?alubalantar lamarin

Related posts

Leave a Comment