Kotun Kolin tarayya ta tabbatar da Sanata Ahmad Lawan matsayin halastaccen ?an takarar kujerar sanata ta Yobe ta arewa.
Da yake yanke hukuncin al?alin kotun mai shari’a Centus Nweze ya ce Bashir Machina ya gaza gabatar wa babbar kotun tarayya da ke Damaturu hujjar – baka ta zargin aikata magu?i a za?en fitar da gwanin – da ya sa ake gayyatar ?angaren Ahmad Lawan zuwa kotun.
Jam’iyyar APC ce dai ta ?alubalanci Bashir Machina a matsayin ?an takararta na kujerar sanatan Yobe ta Arewa, tana mai cewa Ahmad Lawan ta sani a matsayin halastaccen ?an takara.
A zaman sauraron ?arar da ya gabata, lauyan jam’iyyar Sepiribo Peters ya ce za?en fitar da gwanin da ya bai wa machina nasara, ya sa?a wa dokar za?e ta 2022.
Peters ya ce ba jam’iyyar ce ta na?a Danjuma Manga a matsayin jami’in da ya jagoranci za?en fitar da gwanin ba.
Ya shaida wa kotun cewa jam’iyyar APC ta soke za?en fitar da gwanin sakamakon matsalolin da aka samu a lokacin gudanar da za?en, inda a cewarsa kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya sake shirya wani za?en fitar da gwanin ranar 9 ga watan Yuni, inda kuma Ahmad Lawan ya yi nasara.
To sai dai lauyan Bashir Machina Sarafa Yusuf ya ce Shugaban Majalisar Dattawan bai ?alubalanci hukuncin da kotunan baya suka yi ba.
Ya ?ara da cewa mutumin da ya jagorancin za?en da ya bai wa machina nasara mamba ne a kwamitin gudanarwar jam’iyyar, wanda kuma aka na?a domin ya jagoranci za?en fitar da gwanin.
Sanata Ahmad lawan dai bai shiga takarar fitar da gwani na farko da jam’iyyar ta gudanarar ranar 28 ga watan Mayun 2022, kasancewar ya shiga takarar shugabancin ?asar.
