Kotu Ta Rushe Shugabancin APC Bangaren Ganduje

Wata kotun tarayya dake Abuja, a ?ar?ashin jagorancin Hamza Muazu ta rushe za?en shugabancin jam’iyar APC da tsagin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya gudanar.

Haka kuma mai shari’ar ya tabbatar da za?en da tsagin tshohon gwamnan Kano Ibrahim shekarau ya gudanar.

An ruwaito cewar mai shari’ar ya ce za?en na ?angaren Shekarau, wanda Haruna ?anzago ya lashe, ya samu sanya hannun mutum 7 daga cikin wa?anda uwar jam’iyyar ta turo jihar Kano domin gudanar da za?en.

Alkalin kotun, Mai shari’a Hamza Muazu yace ya amince da zaben da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau suka gudanar.

Alkalin ya yanke hukuncin cewa bangaren Shekarau mai taken G-7 ya gudanar da zaben wanda kwamitin mutane 7 na APC ya sanya wa hannu.

An ruwaito cewa wa?anda su ka shigar da ?ara sun ha?a da Muntaka Bala Sulaiman da mambobin jam’iyyar 17,980, yayin da wa?anda a ke ?arar su ne APC, a matsayin wanda ake kara na ?aya, Mai Mala Buni, shugaban rio, Sen. John Akpanudoedehe sakataren jam’iyyar na ?asa da kuma Hukumar Za?e ta ?asa, INEC.

Kotun ta ce duk taron da ?angaren Ibrahim Shekarau ya jagoranta sahihine.

Nuraini Jimoh, SAN shi ne lauyan Masu Kara yayin da Sule Usman, SAN, M.N. Duru da Mashood Alabelewe Suka kasance Lauyoyin Wa?anda ake Kara.

Related posts

Leave a Comment