Kotu Ta Daure Dan Marigayi Shehu ‘Yar’aduwa A Adamawa

Wata Kotu a jihar Adamawa ta daure dan tsohon mataimakin shugaban kasa zamanin mulkin Soja Marigayi Shehu Musa ‘Yaradua, me suna me suna Aminu ‘Yar’adua.

Kotun dake da zama a Yola, Jihar Adamawa ta daureshine a jiya, Alhamis.

An daureshi ne saboda kashe mutane 4 a wani hadarin mota da ya sameshi, An gurfanar dashine a gaban kotu ne saboda zargin tukin ganganci da yake yi wadda yayi sanadiyar kashe mutanen.

Aminu na karatu ne a jami’ar AUN dake Yola. Wadannan ya kashe din sune Aisha Mamadu, Suleiman Abubakar, da Jummai Abubaka, wanda ciki hadda dan karamin yaro. Sai kuma mutane biyu da suka jikkata Annu da Hajara Aliyu.

Da ake karanto masa laifinsa a Kotu, an bayyana cewa, iyalan 3 daga cikin wanda ya kashe din sun nemi a biya diyyar Miliyan 15. Saidai Aminu ya karyata zargin da ake masa inda yace sharrine. Alkalin Kotun dai ya dage sauraren karar sai zuwa 19 ga watan Augusta.

A lokacin da hadarin ya faru, Rahotanni sun bayyana cewa, da Kyar Aminu ya tsira saboda jama ar gari sun so kasheshi.

Related posts

Leave a Comment