Komawar Jonathan APC Babban Abin Mamaki Ne – Gwamnan Ebonyi

Gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi, ya ce idan har tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya koma jam’iyyar APC, labarin zai zama babban abin mamaki da zai shiga littafin tarihin duniya.

A ranar Litinin, hadakar kungiyoyin arewa su ka siya wa tsohon shugaban kasar fom din takara karkashin jam’iyyar APC, inda su ka bukaci ya tsaya takara a shekarar za?e ta 2023.

Yayin da Umahi ya ke jawabi a gidan gwamnatin jihar ranar Talata, Ya ce an sayi fom din ne musamman don a tozarta Jonathan a babbar shekarar za?e ta 2023.

Yayin jawabi dangane da halin da Jonathan ya ke, Umahi ya ce abu mai wahala ne jam’iyya mai mulki ta yi wa tsohon shugaba kasar kamfen ballantana har ya samu wata nasara.

“Jonathan uba ne a wurina kuma Ubangiji ya yi amfani da shi da matarsa inda su ka mayar da ni gwamna. Don haka duk wanda ya kyautata min, ina girmama shi har abada, tare da matarsa da su taimaka min wurin cika buri na.

“Ba na manta wadanda su ka taimaka mana amma batun komawarsa APC, ba ni da abubuwa da yawa da zan ce amma akwai rubuce-rubuce da dama da na gani. Idan har ya shiga jam’iyyar to wannan zai zama abin al’ajabin da ya faru a wannan karnin.”

Related posts

Leave a Comment