Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi Allah wadai da yankan ragon da yan ta’adda suka yi wa manoma 43 a yankin Zabarmari na jihar Borno.
Jam’iyyar ta ce “ Buhari ya gaggauta zuwa Zabarmari a jihar Borno domin jajantawa mutanen Borno da yan uwan wadanda aka kashe, sannan ya kuma jagoranci yakin tabbatar da tsaro da yankin.”
Jamm’iyyar ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da ta fitar a yammacin yau. Jam’iyyar PDP ta jajantawa al’ummar jihar Borno tare da bayyana irin ta’addancin mayakan boko haram a matsayin zalunci, wanda ta ce dole a dauki matakin kare aukuwar hakan nan gaba.
Wannan kadai ya kara nuna gazawar gwamnatin Buhari na tabbatar da tsaron kasa da rayuka da kuma dukiya a kasarmu.” In ji PDP.
PDP ta ce ta damu kan gazawar gwamnatin Buhari na kasa daukar kwakkwaran mataki duk da koke-koken gwamnan Borno Babagana Zulum kan matsalar tsaro a jiharsa.
