?an takarar gwamnan Jihar Gombe a ?ar?ashin jam’iyyar NNPP, Khamisu Ahmad Mailantarki, ya yi wa Kiristocin Jihar Gombe watandar kayan abinci domin sau?a?a masu wadatar abinci a lokacin Kirsimeti.
Kayayyakin abincin wa?anda aka raba kwana ?aya kafin ranar Kirsimeti, sun ha?a da shinkafa, man girki da kuma tallafin ku?a?e.
An raba kayan ga coci-coci, Kungiyar Kiristoci ta ?asa (CAN) reshen Jihar Bauchi da sauran ?ungiyoyin Kiristoci na cikin jihar.
Da ya ke rabon kayan abincin a ranar Asabar a Gombe, Mailantarki ya ce wannan ?o?ari da ya yi, ya yi ne domin ya sau?a?a masu gudanar da Kirsimeti ba cikin halin damuwa ba.
Daga nan ya ro?e da su yi koyi da Annabi Isa (AS). Ya ?ara da cewa lokacin Kirsimeti, lokaci ne da jama’a za su ?ara himma wajen ?ara kusantuwa da Ubangiji, tare da fatan su ga ?asar nan ta wanzu cikin yanayin da jama’ar ta za su yi rayuwa mai kyakkyawan tasiri.
Sannan ya ro?i Kiristoci su yi koyi da Annabi Isa (AS) wajen nuna ?auna, ha?in kan al’umma da kyakkyawar mu’amalar zamantakewa.
Mailantarki ya ce abu ne da kowa ya sani cewa babu ?asar da za ta iya ci gaba har ta bun?asa, ba tare da an zauna lafiya da juna ba, cikin kyakkwar zamantakewa
Daga nan ya ro?i ‘yan Jihar Gombe su fito su yi tururuwar za?en shugabanni nagari.
Ya ce idan aka zabe shi, ya sha alwashin bunkasa jihar sosai fiye da yadda ya ke a yanzu, nesa ba kusa ba.
