Kirsimeti: Ba Zan Sauka Daga Mulki Ba Sai Na Cika Alkawuran Da Na Yi – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi watsi da duk alkawuran da ta yi ba lokacin yakin neman za?e kafin cikar wa’adinsa.

Shugaban ya bayyana haka ne a sakonsa na Kirsimeti ga ’yan Najeriya, inda ya ce yana taya Kiristoci a Najeriya farin ciki kamar sauran mabiya a duniya don gudanar da bikin a wannan shekarar.

A cikin sa?on, shugaban ya ro?i ?an Najeriya su yi rigakafin korona domin rage bazuwar annobar.

Ya kuma ta?o batun tsaro inda ya ce duk da nasarorin da jami’an tsaro suka samu amma har yanzu akwai ?alubale.

“Ina kira ga ?an Najeriya da su yi imani da mu da kuma ?aukar abubuwan da ke faruwa a matsayin wani lokaci da kuma zai wuce, kamar sauran yanayi marar da?i a tarihin ?asar.”

“Wannan gwamnatin ba za ta yi watsi da al?awullan da ta yi wa ?an Najeriya ba,” in ji shugaban.

Related posts

Leave a Comment