Kimanin Matasa 2000 Ne Za Su Samu Aiki ?ar?ashin Bizi Mobile

An ?iyasta cewa kimanin Matasa 2000 ne zasu samu gajiyar aikin Banki da Kamfanin Bizi Mobile, kamfanin da ya saba hada hadar ku?i ta zamani.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban Kamfanin Alhaji Aminu Bizi, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da yayi a Kaduna.

Bizi ya bayyana cewar tuni kamfanin nashi bisa ga ha?in gwiwa da babban Bankin Najeriya,suka cimma wata matsaya na inganta rayuwar matasa da magance matsalar zaman banza, kuma kamfanin nashi ya bada fifiko sosai a yankin Arewacin Najeriya, kasancewar yankin na koma baya ta wannan bangare.

Hakazalika Kamfanin na Bizi ya shirya wasan ?wallon kwando ga matasa domin kara jawo su jika, sannan Bankuna ne ake sa ran zasu ?auki nauyin gasar, domin wadannan Matasa ne ake sa ran Kamfanin zai dauka aiki.

Matasan zasu dawo unguwanni da ?auyukan su domin cigaba da bu?e asusun banki ga jama’a da samar da katin ATM ga jama’a, yadda jama’a musamman al’ummar Arewa zasu amfana sosai.

Related posts

Leave a Comment