Rahotanni daga jihar Kebbi na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro a kalla 19 a wani hari da suka kai a ?auyen Kanya da ke cikin karamar hukumar Danko-Wassagu.
Maharan sun je ne a kan babura a lokacin da mataimakin gwamnan Kebbi ke ziyara a ?auyen a ranar Talata.
Mataimakin gwamnan Samaila Yombe Dabai, ya shaida cewa dakarun tsaron sun fafata ne da maharan, amma bai fa?i yawan jami’an da aka kashe ba.
Mutanen da suka mutun sun ha?a da sojoji 13 da ?an sanda biyar da wani ?an sa kai.
Maharan sun kuma sace kayan abinci da dabbobi.
Harin ya faru ne kwana ?aya bayan da ?an bindiga suka kashe ?an sa kai 63 a yankin.
