Rahotanni daga jihar Kebbi sun bayyana cewa akalla mutane 160 ne suka nutse a cikin ruwa ciki har da mata da kana nan yara sakamakon nutsewar Wani jirgi da ya taso daga jihar Niger.
Jirgin wanda ya taso daga jihar Niger ya samu matsala ne da misalin karfe 10 na safiyar yau Laraba a lokacin da yake daf da zuwa garin da zai tsaya a garin Wara dake jihar.
A cewar shaidun gani da ido, jirgin ya dauko kusan ninkin adadin da yakamata ya dauka saboda mutum 65 zuwa 80 aka tsara zai dinga dauka amma aka zuba masa mutane 160 tare da buhuhhunan yashi.
Tuni Abdullahi Buhari, shugaban karamar hukumar Ngwaski, ya je bakin ruwan inda ake ake aikin ceto mutanen da suka nutse.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa kawai wasu mutum takwas ‘yan gida daya da lamarin ya rutsa dasu.
