Rahotanni daga Jihar Kebbi na bayyana cewar ?an bindiga sun kashe wasu mutane harda ?an sanda da sojoji a ciki a karamar hukumar Danko Wasagu, jihar Kebbi.
Kakakin ?an sandan jihar ya bayyana cewa maharan sun kashe sojoji biyu da ?an sanda ?aya sannan da wasu mutane 13 a ?auyen ?ankade dake karamar hukumar Danko Wasagu.
Bayan haka ya ?aryata rahotannin da ake ta ya?awa cewa wai mutum sama da 50 ne mahara suka kashe.
” Maharan da suka aikata wannan abu sun shigo ne daga Zamfara. Amma kuma suma ba su ji da da?i ba domin dakarun mu sun ragargaje su. An kashe ?an bindiga da dama duk da dai sun kashe sojoji biyu da ?an sanda ?aya.
Jihar Kebbi ita ma tana fama da hare-haren ?an bindiga matuka, domin a cikin shekarar da ta gabata ?an bindiga suka sace daliban makaranta.
