Kebbi: An Damke Inyamurin Da Ya Dirka Wa Bahaushiya Ciki


An tasa keyar wani dan kasuwa mai suna Onyebuchi Okafor da wata budurwa mai suna Mansura Shehu gidan kaso don aikata zina wanda hakan ya jawo samun ciki a tsakaninsu har sai ranar 5 ga wannan wata inda za a ci gaba da sauraron karar.

‘Yan sanda ne suka gabatar da su a kotun magistiri ta Samaila Kakale Mungadi da ke Birnin Kebbi.

Iyamurai dai sun taso inda suke goyon bayan sai dai a ba da belin Okafor amma wasu Hausawa sun ce dole ne a yi mashi irin hukunci da aka yi Yunusa Yellow.

Wani Shugaban al’umma a Birnin Kebbi, Alhaji Yakubu Ahmed ya ce za su hada karfi da karfe su ga wannan mutumin bai ci bulus ba.

Related posts

Leave a Comment