Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Faskari

?an bindiga sun kai mummunan hari ?auyen Shau a ?aramar hukumar Faskari ta jihar Katsina a ranar Lahadi inda suka kashe a ?alla mutum takwas.

Mazauna garin sun ce ?an bindigan sun ?one gidaje masu yawa a kauyen sannan sun sace kayan abinci da wasu kayyakin biyan bu?atu. A

An ruwaito cewa ?an bindigan har ila yau sun lalata motar dagajin ?auyen, dalilin harin ya saka mutane da dama sun tsere zuwa ?auyukan da ke makwabtaka da su.

Jami’an tsaro na ha?in gwiwa da suka amsa kirar mazauna ?auyen sun yi bata kashi da ?an bindigan sun kora su cikin daji.

Mai magana da yawun rundunar ?an sandan jihar Katsina, SP Isah Gambo ya tabbatar da afkuwar harin.

Related posts

Leave a Comment