Labarin dake shigo mana daga cikin garin Katsina na tabbar da cewa wasu ?an bindiga ?auke da muggan makamai sun kai samame a wasu Unguwannin cikin birnin na Katsina.
Wuraren da suka ?addamar da harin sun ?unshi Sokoto Rima wajen Difiri, da bayan KTTV Inda ake kyautata zaton cewa sun ?auki Mutane Bakwai tare da tafiya dasu.
Mai Magana da Yawun Rundunar ?an Sandan Jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbar da kai harin, Inda ya bayyana cewa Maharan sun kai samame ne da misalin ?arfe biyu da rabi na daren ranar 22/06/2022 ?auke da bindigu ?irar AK 47.
?an Ta’adar sun kai hari ne a Gidan wani ?an Kasuwa mai suna Abdullahi Esha, a Unguwar Sokoto Rima anan Katsina sunyi awon gaba da Matar shi ?ar kimanin Shekaru Goma Sha Takwas (18).
Sai dai sashen Rundunar ?ansandan mai kai ?aukin gaugawa akan ayyukan Garkuwa da Mutane sun amsa kiran gaugawa, Inda suka mai da farmakin maharan tare da Ku?utar da Yarinyar mai suna Walida Abdulaziz Maigoro, ba tare da rauni ba, a yayinda su kayi nasarar korar maharan.
Bisa ga dukkan Alamu dai ?arayin sun latsa sunga Jini, tun suna zuwa ?auyukan da suke zagaye da Birnin Katsina har takai ga sun fara shigowa cikin Gari, ko a Satin da ya gabata sai da Maharan suka kai wani harin tare da ?aukar Mutane suka nemi ku?in fansa.
