Katsina: Motocin Kwastam Sun Murkushe Mutum 7 A Kokarin Kamo ‘Yan Sumogal

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Motocin sintiri na hukumar kwastam ta Najeriya sun murkushe mutane bakwai har lahira, ciki har da wata yarinya ‘yar shekara 13 a kan babbar hanyar Jibia zuwa Kauran.

An tattaro cewa akalla mutane 19 ne suka samu munanan raunuka, Wani mazaunin yankin Abubakar Jibia ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe lokacin da jami’an Kwastam da ke aikin sintirin su ke bin mota kirar J5 Peugeot da ake zargin tana dauke da haramtattun kayayyaki.

Abubakar Jibia ya shaidawa majiyarmu cewa wadanda abin ya rutsa da su da ake kyautata zaton manoma ne suna tsaye a bakin hanya ne lokacin da motar sintirin ta kauce daga kan babbar hanya ta buge su ta murkushe su nan take suka ce ga garinku nan.

Wani shaidan gani da ido, Usman Kabir, ya ce: “Motar sintiri da motar ‘yan fasa kwabri suna gudu kan hanyarsu ta zuwa garin Jibia ne kawai direban motar sintirin ya kauce daga kan hanya ya bi ta kan mutane.

“Mutane shida sun mutu nan take, daya ya mutu yayin da aka garzaya da shi a Babban Asibiti na Amadi Orthopedic Katsina, yayin da sauran 19 da suka samu raunuka yanzu haka suke kwance a asibitin.”

‘Yan fasa kwabri sun tsere, an kone motar jami’an kwastam Majiya ta bayyana cewa masu fasa kwabrin sun tsere yayin da fusatattun mutane a wurin da lamarin ya faru suka kona motar jami’an kwastam din kafin isowar jami’an tsaro da suka takaita hargitsin.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ta kwastam a jihar Katsina, Danbaba Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce tuni aka fara gudanar da bincike don gano yadda lamarin ya faru.

Related posts

Leave a Comment