A cigaba da tattaunawar da wakilinmu ke yi da wasu daga cikin mutanen da ‘yan bindigar suka sace kuma gwamnatin jihar Katsina ta kubutar da su. Malam Abubakarub, shi ne Maigarin Unguwar Malamai, da ke gundumar Yantumaki, a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun zo ne garin ne da bindigogi, inda suka dauke ni da mata da kananan yara goma sha shidda har da na goye.
Maigarin Unguwar Malamai ya bayyana haka ne, jim kadan bayan ziyarar bankwana da sakataren gwamnati jihar Katsina, ya kai masu a sansanin yan yiwa kasa hidima dake hanyar Mani cikin garin Katsina, inda aka ajiye su bayan gwamnati jihar Katsina ta kubutar da su, kafin a hannanta su ga shugabanni kananan hukumomi da suka fito.
Basaraken ya ci gaba da cewa gaskiya na ga tasku, amma mun ga abubuwan da ko dirama sai haka, abinci dai sau guda zaa ba ka shi, tuwo ne dan kadan, ruwa ma sau Daya za ka sha. Kamar ni da Shugaba, suna jika ni da ruwa sanyi duk dare, kuma a waje ni ke kwana, matan kuma suna cikin bukka, babu mayafi ga jikani ciki yashi ne.
Shekaran jiya tun da safe suka ce mu fito an yi sulhu da gwamnati, gaskiya mun ji dadi da aka kubutar da mu. Ina da mata biyu da yara goma sha ukku
