Fusatattun mazauna kauyen Wurma a karamar hukumar Kurfi sun tsohe babban titin Katsina-Dutsinma kan hare-haren ?an bindiga Masu zanga-zangar sun hana matafiya wucewa, lamarin da ya tilasta wa ababen hawa canza hanya domin tafiya garuruwan da suka nufa a sassan jihar Mai magana da yawun rundunar ?an sandan jihar, ASP Aliyu, ya ce zai tuntu?i DPO na Kurfi gabanin ya yi magana a hukumance
Jihar Katsina – Mutanen kauyen Wurma a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina sun fara ?one-?one tare da toshe babban titin Katsina-Dutsinma ranar Jumu’a, 1 ga watan Maris. Mazauna kauyen sun toshe titin ne domin nuna fushinsu kan yadda ?an bindiga suka matsa musu da kai hare-haren ta’addanci da kashe-kashen rayuka.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa zanga-zangar da tilastawa motoci da sauran matafiya canza hanya, sun koma bin hanyoyin jeji da suka ha?a Dutsinma da sassan Katsina.
Wani mai suna, Abdulkarim, ?aya daga cikin ?an kauyen da suka fito zanga-zanga ya ce a kwanaki hudu da suka shiga, ?an bindiga suna shiga garinsu ba ?aga ?afa. A cewarsa, hare-haren ta’addanci da ?an bindiga ke yawan kai musu ga jefa su cikin rayuwar tsoro da fargabar abin ka iya faruwa a ko wane lokaci.
Yayin da aka tuntu?i kakakin rundunar ?an sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu, ya ce zai nemi ?arin bayani daga DPO na Kurfi kafin ya yi magana. Sai dai har zuwa lokacin da muka ha?a muku wannan rahoton, ba a samu wani karin bayani kan lamarin ba daga rundunar ?an sanda.
Haka nan kuma har zuwa misalin karfe 2:00 na rana, jami’an tsaron da suka je wurin ba su taka kara sun karya ba, kamar yadda Daily Post ta rahoto. Fusatattun mazauna kauyen sun yi amfani da wannan dama wajen hana ababen hawa wucewa da tilastawa matafiya canza hanya.
