Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya dauki sabon salo da nufin kawo karshen matsalar rashin tsaro da ke addabar mutanensa. Bayanan da mu ka samu sun ce Mai girma Gwamnan zai tura kudiri zuwa majalisar dokokin jiha da zai taimaka a wajen samun karin jami’an tsaro.
Babban mai taimakawa Gwamnan a dandalin sada zumunta, Isa Miqdad ya shaida cewa kudirin zai bada damar kafa Katsina Community Watch wadda za ta samu alhakin daukar mazauna garuruwa aikin tsaro a fadin jihar Katsina.
Kamar yadda hadimin ya bayyana, za a horas da wadannan mutane, kuma a ba su manyan makamai domin su tunkari ‘yan bindigan da suke yin ta’addanci a fadin Jihar.
