Katsina: An Ceto Mai Gari Da Jama’arshi Daga Hannun ‘Yan Bindiga

Jami’an tsaro a jahar Katsina sun yi nasarar ceto wasu mutane 9 da masu satar mutane suka yi garkuwa da su.

Mutanen 9 sun hada da maza 5 ciki har da yaron goye da kuma mata 4 wadanda suka ce an sato su ne daga kauyen Bima dake kasar Nijar.

Gwamna Aminu Masari ya karbi mutanen a gidan gwamnatin jahar Katsina a ranar Litinin dinnan daga hannun jami’an tsaron a karkashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sandan jahar, CP Sanusi Buba.

Mai Garin Bima, Sama’ila Ali, na daga cikin wadanda aka kubutar din, kuma ya bayyana wa manema labarai cewa kwanaki 9 suka yi a hannun masu garkuwar.

Shi ma da yake bayani, wani dattijo dake cikinsu mai suna Usman Sha’aibu ya ce sun sha duka kuma ga yunwa domin kuwa dan abincin da ake basu bai taka kara ya karya ba.

Gwamna Masari, a sa’ilin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida jim kadan bayan amsar mutanen da aka kubutar , ya musanta zargin da ake yi na cewa wai ya koma yin sasanci da ‘yan ta’adda a jahar

Related posts

Leave a Comment