Labarin dake shigo mana da ?umi-?umi daga ?aramar Hukumar ?an?ara ta jihar Katsina na bayyana cewa ?aruruwan ?aliban da wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su daga wata makarantar sakandire ta kimiyya da ke karamar hukumar ?an?ara a jihar Katsina sun dawo.
A bayyana cewar ?aliban sun dawo ne bayan sun shafe tsawon dare a cikin wani jeji a safiyar yau Asabar, 12 ga watan Disamba, bayan tattara su da ‘Yan Bindigar suka yi da asubahin wannan rana ta Asabar.
Jaridar Legit.hausa ta ruwaito cewa mafi akasarin daliban da aka gano suna samun kulawar likitoci sakamakon samunsu da aka yi da raunuka daban-daban.
Da dama daga cikin wadanda aka gano na samun kulawar likitoci na wasu raunuka daban-daban da suka samu.
Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan bindigar sun shiga har dakin kwanan daliban tare da yin awon gaba da su da duku-dukun safiyar yau, Asabar.
