Kashi 70 Na Yara ‘Yan Firamare A Najeriya Dakikai Ne – UNICEF

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Asusun lamunin yara na majalisar dinkin duniya watau UNICEF ya ce kashi 70 cikin 100 na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai da ake koya musu a makaranta.

Masanin sadarwa na UNICEF, Mr Geoffrey Njoku, ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a jihar Kano lokacin taron tattaunawa da manema labarai kan shirin bunkasa ilimin yara na majalisar dinkin duniya.

Ya bayyana cewar makasudin zuwan yara makaranta a farkon lokaci shine domin iya rubutu da kuma lissafi, sai dai abin damuwa shine yadda hakan ya gagara samu a mafi yawan yara.

“Tun 2010, mun yi kokarin magance matsalar yara milyan 10.5 da basu zuwa makaranta, amma duk da haka kashi 70% na yaran dake makarantar basu fahimtar darasi.”

“Ya kamata mu hada adadin kashi 70% din nan kan milyan 10.5 da basu zuwa makaranta gaba daya don a maida hankali sosai kan lamarin.”

Related posts

Leave a Comment