Kasafin Ku?in INEC: Rikici Ya ?arke A Majalisa

A ranar Laraba hu?u ga watan Nuwamban shekara ta 2020 ne shugaban Hukumar za?e mai zaman kanta INEC Farfesa Mahmoud Yakubu tare da tawagarsa suka gabatar da kasafin 2021 a gaban Majalisar ?asa.

Bayan soma gabatar da jawabin Shugaban na INEC ne, wani ?an kwamitin INEC, Solomon Bob yayi yunkurin dakatar da shi, inda tarayyar ‘yan Kwamitin INEC a majalisa suka ?i amincewa da kasafin Hukumar, da Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya gabatar a kan ayyukan hukumar a 2020.

Majalisar dattawa sun bukaci zantawar sirri tsakanin su da shugaban INEC din ba tare da tawagarsa ba, dangane da kasafin.

Bayan shugaban kwamitin, Aishatu Jibril Dukku ta bukaci Yakubu da ya bayar da bayanin kasafin 2020, sannan ya gabatar da kasafin 2021, sai dai kafin ta kai ga karasawa abokin aikinta, Hon. Solomon Bob daga jihar Rivers, ya katse ta, inda yace kwamitin ba su riga sun yi wata kididdiga ba ta wannan shekarar, ga shi kuma ana bukatar a gabatar da na shekara mai zuwa.

Dukku tayi ta kokarin yin bayanin cewa kullen COVID-19 ne ya lalata duk wani shirinsu, amma Bob ya ki barinta ta kai aya. Take a nan ran Dukku ya baci, tace masa “Mai girma abokin aikina, ina bukatar kayi shiru,” inda ta bukaci Yakubu ya fara jawabin.

Saboda wannan dalilin ne aka bukaci duk ‘yan kwamiti su fita, a yi magana da shugaban INEC.

Related posts

Leave a Comment