Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar shugaban kasa ta ce Babban Bankin ?asar ba shi da wani dalili na ?in bin umarnin Kotun ?oli kan sabbin takardun ku?i don fakewa da sunan jiran umarni daga Shugaba Muhammadu Buhari.
Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafafen ya?a labarai, Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa inda ya ce Shugaban ?asar bai umarci atoni janar na ?asa, Abubakar Malami da Gwamnan CBN, Godwin Emiefele su ?i martaba umarnin kotu ba da ya shafi gwamnati da wasu ?angarorin.
A ranar 3 ga watan Maris ne Kotun ?olin ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun ?udi har zuwa 31 ga watan Disamban bana.
Umarnin kuma ya zo ne bayan da gwamnonin jihohi 16 suka ?alubalanci matakin sauya fasalin ku?in.
Jihohi 16 ?ar?ashin jagorancin Kaduna da Kogi da Zamfara sun bu?aci kotun ?olin ta soke matakin gwamnatin bisa dalilan cewa hakan ya jefa ?an Najeriya cikin ?unci da wahala.
Kotun ta ?ara da cewa rashin martaba umarnin kotun na ranar 8 ga watan Fabrairu, alama ce ta mulkin kama-karya inda ta bayyana cewa shugaban ya sa?a wa Kundin tsarin mulkin ?asa a yadda ya bai wa CBN umarnin sake fasalta ku?in ?asar.
Sanarwar dai ta ce Shugaban ?asar babban mai mutunta dokoki ne kuma babu adalci a yadda ake yi sukar Shugaban da yi masa mummunan zato.
