Kano: Wata Mata Ta Yi Wa Kanta Yankan Rago

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wata mata da ake zargin ta kashe kanta a unguwar Sheka da ke ?aramar Hukumar Kumbotso.

‘Yan sandan dai sun ce matar ta kashe kanta ne ta hanyar amfani da wani fasasshen gilashin taga, inda ta yanka kanta bayan gartsa wa mahaifinta cizo sannan ta gutsire dan yatsanta da ke ciwo.

A cewar dan uwan marigayiyar mai suna Muhammad Sanusi, kafin ‘yar uwar tasu ta kashe kanta ta yi fama da ciwon yatsa wato karkare, wanda har sai da ta kai ga sun rufe ta a ?aki na tsawon kwana biyar, sakamakon yadda ta koma tamkar mai ta?in hankali.

Ya ?ara da cewa a ranar da suka bu?e ta ne ta fasa gilashin tagar ?akin da aka rufe ta sannan ta yanka kanta a makogoro.

A shekarar 2021 an samu mutane sama da biyar da suka kashe kansu a Kano da ke arewacin Najeriya, wanda wasu daga cikinsu aka ala?anta da matsalar ?wa?walwa.

Na baya-bayan da aka samu shi ne na wani matashi da ya kashe kan sa ta hanyar yanke al’aurar sa.

Related posts

Leave a Comment