Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar wata kotun majistiret dake zamanta a Kano, ta hana Matashin da ake zargi da yiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, batanci rubutu a dandalin Facebook.
Kotun ta ?auki wannan matakin ne a zamanta na ranar Litinin, 8 ga watan Nuwamba, 2021 yayin zaman cigaba da sauraron ?arar.
BBC Hausa ta buga a shafinta na Facebook cewa Alkalin kotun, Mai shari’a Aminu Gabari, ya kuma janye belin da ya baiwa wanda ake zargin, Muazu Magaji Danbala kiru.
Alkalin ya ?auki matakin janye belin ne biyo bayan gaza cika sharu??an da aka gindaya masa, kuma lauyansa ya nuna cewa sharu??an sun yi tsauri.
Shugaban ?aramar hukumar Nasarawa dake cikin kwaryan birnin Kano, Auwalu Aramfo, shine ya kai karar mutunen biyu, Muazu Magaji Danbala da kuma Jamilu Shehu.
Honorabul Aramfo ya garzaya gaban hukumar tsaro ta farin kaya yana neman a kwatar wa gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ha??insa kan mutanen. A cewarsa wa?anda ake zargin sun bata wa gwamna suna da kuma wasu daga cikin iyalansa a shafin sada zumunta ta hanyar kiransu da barayi, masu karkatar da ku?a?en al’umma.
Bayan sauraron ?arar a yau Litinin, Mai shari’a Aminu Gambari, ya ?age sauraron shari’ar har zuwa ranar 29 ga watan Nuwamba, 2021.
