Kano: Majalisar Malamai Ta Yi Kiran A Dakatar Da Gina Masallatai A Jihar

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Majalisar Malamai ta ?asa reshen jihar ta bayyana dalilanta na yin kira a rage gina Masallatai barkatai a jihar.

A wata sanarwa da ta fitar bayan wani babban taron da ta gudanar na kwana biyu a ?arshen makon da ya gabata a Kano, majalisar ta bayyana jerin sharwari da manufofin da ta cimma a wajen taron, kuma ciki har da rage yawan bu?e masallatai.

“A rage bu?e masallatai barkatai domin guje wa rarraba kai da zukatan al’umma,” a cewar sanarwar da majalisar malaman ta fitar bayan kammala taron,

Amma cikin sanarwar, an yi kira ga malamai da limamai su dinga raya masallatai da karatuttuka da lakcoci baya ga tsayar da sallah a cikinsu.

Taron na ha?in gwiwa da Sashen Nazarin Addinin Musulunci da Shari’a na Jami’ar Bayero, ya ?unshi wakilai na malamai da limamai na ?ananan hukumomin jihar Kano 44 da shugaban Jami’ar Bayero da wakilcin Kwamishinan Lamuran Addini Dr Muhammad Tahar Adamu.

Majalisar Malaman ta ce taronta ya mayar da hankali ne kan gudunmawar malamai da limamai wajen samar da tarbiya da inganta zaman lafiya da dora al’amura bisa tushen shari’ar Musulunci.

Kuma an gabatar da ma?aloli tare da yin ta’aliki kan makalolin da aka gabatar. Daga cikin matsayar da taron ya cimma, majalisar malaman ta ce “yin haka zai inganta zaman lafiya a ?asa baki ?aya.”

Sanarwar ta ?ara da cewa mahalarta taron sun yi takaicin yadda wasu malamai suke zubar da dajararsu ta hanyar yadda “suke bin ?an siyasa suna masu yin biyayya.”

Haka kuma malaman na Kano sun ce akwai wasu bara-gurbin malamai da ke haddasa rikici da rarrabuwar kai a cikin majalisar malamai domin cimma burinsu na kashin kansu.

Majalaisar malaman ta ce malamai da limamai sun bayar da gudunmawa mai yawa a tarihin musulunci wajen jagorantar al’umma game da tarbiyya da shugabanci na gari da zaman lafiya da samar da tsaro

“Wannan ya sumu ne ta hanyar kyawawan dabi’u da ta?awa da tawali’u da gaskiya da magabata a cikin malamai da limamai da suka siffatu da ?ora al’umma kan biyayya da shugabanci da ilimi.”

Amma majalisar ta ja hankalin mambobinta kan ha??in da ke kansu na yi wa masu mulki nasiha.

Ta yi kira ga malaman cewa: “A ri?a yi wa masu mulki a kowane mataki nasiha kan nauyin da ke kansu.”

Ta kuma yi kira da a zaburar da matasa da majalisar ta ce – masu tarbiya game da shiga ayyukan tsaro da harkokin siyasa da shugabanci.

Majalisar ta kuma bu?aci malamai da limamai su rika girmamawa da ziyartar junansu domin samar da hadin kai da fahimtar juna domin zaman lafiyar dalibai da sauran al’umma.

Majalisar ta kuma jaddada cewa tana gudanar da ayyukanta ne bisa tsarin doka da aka yi mata rijista, don haka ta ja hankalin mambobinta cewa “babu wanda zai yi mata karfa-karfa ya sa ta yi abin da ya sa?a wa doka da ka’idoji da sharu??anta.”

Related posts

Leave a Comment