Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano ya abawa masu Zanga-zangar kawo karshen matsalar tsaro A Arewa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yaba wa masu zanga-zangar neman da?ile matsalar tsaro bisa aiwatar da ita cikin lumana.
Kwamishinan ‘Yan Sanda Habu Ahmad ne ya tar?i masu zanga-zangar, inda suka mi?a masa bu?atunsu a rubuce.
Kwamishinan ya kar?i bu?atun nasu tare da tabbatar musu da cewa za a mi?a bu?atun nasu ga hukumomin da suka dace.
An shiga rana ta biyu kenan da Gamayyar Kungiyoyin Arewa suka kira yin Zanga-zangar gama gari a fadin Arewa, domin kawo karshen yawaitar kashe-kashen da ke faruwa a yankin.
