A ranar Laraba ne wata kotu a Kano ta soke belin da aka bai wa fitaccen mawa?in nan Naziru Ahmed Sarkin Wa?a, inda ta gindaya wasu sababbin sharu??an belin.
Sai dai kotun ta ri?e Naziru inda ta aike shi gidan yari saboda rashin cika sharu??an a kan lokaci, duk da cewa an gindaya shara??un ne a ranar Larabar.
Ana ?arar Naziru ne dai kan cewa ya saki wata wa?a ba tare da hukumar tace fina-finai ta Kano ta tantance ba.
Sharu??an sun ha?a da cewa sai ya kawo wani Maigari da zai tsaya masa da kuma Kwamandan Hizbah na ?aramar hukuma a matsayin sharu??an beli.
Wani makunsancinsa ya ce sun cika sharu??an, sai dai kuma ba a samu kai wa ga al?alin da zai bayar da umarnin ba da belin ba.
A watan Satumban 2019 ne aka fara kama Naziru Sarkin Wa?a amma daga bisani kotun majistare da aka kai shi ta sake shi bayan ya cika sharudan belin da kotun ta yanka masa.
