Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar wata kotu da ke zamanta a Nomansland ta bada umurnin a tsare wani Matashi mai suna Mu’azu Magaji Danbala saboda ta?a mutuncin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Ana tuhumar wanda ake zargin ne da furta kalaman cin mutunci ga gwamnan da yaransa biyu; Abdulaziz da Balaraba a shafin sada zumunta na Facebook.
?ayan wanda ake zargin mai suna Jamilu Shehu har yanzu bai shigo hannu ba. An gurfanar da mutanen biyu ne kan hadin baki, zagi da gangan, tada zaune tsaye da ?ata suna wanda hakan sun saba da sashi na 97, 114, 391 da 399 na Penal Code.
A cewar bayanin farko, a ranar 26 ga watan Oktoban 2021, shugaban ?aramar Hukumar Nasarawa, Auwal Lawal Shuaibu ya shigar da korafi wurin hukumar binciken sirri na musamman, SIB, kan mutanen biyun mazauna ?iru a Kano.
Rahoton na farko ya ce: “A ranar da aka ambata da farko, ku biyu kun ha?a baki kun wallafa hotunan mai girma Gwamnan Kano, har da yaransa biyu ?auke da rubutu mai cewa ‘?arayin Kano’ tare da sanin cewa abin da kuka aikata zai iya tada rikici a Kano da wajen Kano. “Don haka ana zargin ku da aikata laifukan da aka ambata tunda farko.”
Sai dai wa?anda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa kuma suka nemi beli. Daga nan kotu ta bada umurnin a tsare mata wanda ake zargin bayan ?in amincewa da bukatarsa ta neman beli.
An dage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Nuwamban 2021.
