Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Kotun Majistire dake zamanta a Nomansland, ta ba da umarnin cigaba da tsare tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Muazu Magaji, a gidan gyaran hali.
An ruwaito cewa an gurfanar da tsohon kwamishinan, wanda aka fi sani da ?an Sarauniya, a gaban kotun bisa zargin bata sunan gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano.
Al?alin Kotun, Mai shari’a Aminu Gabari, shi ne ya baiwa jami’an tsaro umarnin cigaba da tsare ?an Sarauniya a zaman sauraron ?arar da ya gudana yau Litinin.
Haka nan kuma, Alkalin ya ba da umarnin a tura Likitoci na musamman su duba lafiyar wanda ake zargi, wanda ya yi ?aurin suna wajen cacakar Ganduje, a Kano.
Bayan haka, sai mai shari’a Gabari ya ?age sauraron ?arar har zuwa wata mai kamawa, ranar 2 ga watan Fabrairu, 2022. Kazalika ya umarci Lauyoyin bangarorin guda biyu, wanda ake kara da masu shigar da ?ara, su ha?a kundin shari’ar kuma su kai masa a ranar zama na gaba.
