Hukumar Hisbah a Kano ta ce ta kama
mabarata 178 da suka karya dokar hana bara da gwamnatin jihar ta saka.
Babban kwamandan hukumar, Harun Ibn-Sina ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Kano, cewa hukumar ta yi wannan kamen ne daga watan Satumba zuwa Disambar nan.
Yace daga cikin wadanda suka kama akwai mata 102 da maza 76. Ya kara da cewa hukumar za ta cigaba da kamen duk mabaratan da suka yi kunnen kashi game da dokar hana bara ta gwamnatin Kano.
Harkar barace barace dai wata dabi’a ce wadda ta da?e tana ci wa Jihohin Arewa tuwo a kwarya, kuma gwamnatoci a baya da yanzu suna iya kokarin su wajen ganin sun ya?i wannan ?abi’a da ta da?e tana zubar da mutuncin jama’ar Arewa musanman a yankin Kudancin ?asar.
