Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar wata tukunyar gas ta sake fashewa ranar Juma’a a unguwar Sharada ‘yan tagwaye inda ta jikkata mutane da dama.
Rahotanni sun ce da misalin karfe uku na yammacin Juma’ar ne wasu masu aiki walda da suke kokarin fasa tukunyar gas ne suka fasa wata tukunya, abin da ya janyo fashewarta da ta wasu tukunen gas da ke kusa.
Wani wanda abin ya faru a kan idonsa da ake kira Ibrahim Muhammad ya ce “tukunyar gas takwas aka kawo wajen masu waldar da za su iya mayar da su na amfanin gwan-gwan, an yanka bakwai lafiya lau babu komai cikinsu, amma ta takwas din akwai sauran sinadarai a ciki, sai aka ce kada a yanka ta a hakura.
“Bayan tafiyar shugaban wurin sai matashin da ke aikin ya nemi ya ci gaba da yankata, yana yankata sai sinadarin cikin mai launin ruwan dorawa ya fara feshi a sama, in ji Ibrahim.
Shugaban asibitin Murtala Husaini Muhammad ya ce
“Tukunyar gas din da ake fasawa domin a yi gwan-gwan da ita ce ta fashe sai sinadaren da ke cikinta suka rika fantsama mutane na shaka”.
