Kano: APC Ta Dakatar Da ?an Majalisa Mai Sukar Ganduje

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar babbar Jam’iyya mai mulki ta APC reshen Jihar Kano ta dakatar da Hon Sha’aban Ibrahim Sharada, dan majalisar wakilai da ke wakiltan yankin karamar hukumar birni da kewaye na Kano, tsawon shekara guda.

An ruwaito cewa an dakatar da Sharada ne bisa zarginsa da ayyukan da suka saba jam’iyya. An tattaro cewa kwamitin ladabtarwa na mutum bakwai da aka kafa domin binciken zarge-zargen da ake yi masa sun same shi da laifi dumu dumu.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa an haramtawa Sharada shiga dukka harkokin jam’iyyar a dukkan matakai.

“An samu Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada da aikata laifin da ake tuhumarsa da shi na sukan halayyar mai girma Gwamnan Kano da kuma shugabannin jam’iyya daban-daban daga shiyya, Karamar Hukuma da Matakin Jiha.

“Cewa ba zai tsoma baki a dukkan harkokin jam’iyyar da ayyukanta ba a dukkan matakai har na tsawon shekara guda” kamar yadda wasikar da kwamitin ya karanta.

Related posts

Leave a Comment