‘Yan sanda a Kano sun gabatar wa da lauyoyin Injiniya Mu’azu Magaji tuhume-tuhumen da ake yi masa na cin mutuncin Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.
An kama Injiniya Mu’azu ne a Abuja bayan kammala wata tattaunawa da gidan talabijin na Trust TV.
Barista Garzali Datti Ahmad na ?aya daga cikin lauyoyin injiniyan kuma ya fa?a wa BBC cewa daga cikin tuhumar akwai ?ata sunan Gwamna Ganduje da zagin sa da cin mutuncin iyalain sa da yun?urin haddasa tashin hankali.
Baristan ya ?ara da cewa gwamna ne ya kai ?orafi kan Injiniya Mu’azu, wanda shi ne tsohon kwamashinan ayyuka ?ar?ashin mulkin Gandujen.
