Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki ta mika takardar shedar shugabancin jam’iyyar ga bangaren gwamnan jihar Kano, wanda ya zabi Abdullahi Abbas a matsayin sabon shugaba.
Sakataren rikon jam’iyyar na kasa Mista John Akpanudoedehe, ya mika takardar ga Abdullahi Abbas, wanda yake tare da Gwamna Ganduje da dan Majalisar Tarayya Alhassan Ado Doguwa da Kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sulen Garo.
Bayar da takardar shedar ta biyo bayan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta kasar ta yi ne inda ta soke hukuncin babbar kotun da a baya ta ba bangaren tsohon gwamnan jihar Mallam Ibrahim Shekarau nasara a shari’ar shugabancin.
?angaren Shekarau din wanda ke da Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jami’iyyar ya ce zai ?aukaka ?ara kan hukuncin kotun da ya ce shugabancin ?angaren gwamna ne halastacce.
Ahmadu Haruna Zago, ya fa?a wa BBC Hausa cewa za su yi biyayya ga hukuncin amma za su ?aukaka ?ara.
“Za mu ?aukaka ?ara mana, ai bin umarnin daban kuma ?aukaka ?ara daban,” in ji shi. “Lauyoyinmu na nazari kan hukuncin kotun.”
Hakan na nufin Kotun ?oli ce za ta raba gardama idan suka ?aukaka ?arar, kasancewar Kotun ?aukaka ?ara ce ta yi hukuncin na yanzu.
A zaman da ta yi ranar Alhamis a Abuja, Kotun ?aukaka ?arar ta ce Babbar Kotun Abuja ba ta da hurumin yin hukunci kan rikicin sannan kuma ta ce shugabancin Abdullahi Abbas ne halastacce – ba na Haruna Zago ba.
A makon da ya gabata ne bangaren Shekarau ya yi watsi da wani yun?urin sulhu da jam’iyyar ta ?asa ta yi, inda ta na?a Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamatin sasanta rikicin da suke yi.
