Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar ?an takar gwamnan Jihar a Jam’iyar PDP a za?en 2019, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheka daga PDP zuwa NNPP a hukumance.
An ruwaito cewa Yusuf, wanda a ka fi sani da Abba Gida-Gida, ya sanar da sauya she?ar ne a yau Lahadi a maza?arsa ta Diso, ?aramar Hukumar Gwale a Jihar Kano.
A jawabinsa, Yusuf ya ce PDP da APC duk kanwar ja ce, inda ya ce jam’iyar ta ci amanar al’ummar Kano da jagoran ta, tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso duk da irin ?imbin ?uri’ar da su ka ka?a mata a za?en 2019.
A cewar sa, matakin sauya she?ar ya zamto mai muhimmanci duba da irin kiraye-kirayen da miliyoyin al’umma su ke yi na ya sauya jam’iyyar NNPP, wacce ta ke da manufofi na gaskiya na tserar da ?an ?asa da ga mawuyacin halin da su ke ciki.
Sauya she?ar ta Abba Gida-Gida ta zamo sharar hanya ga Kwankwaso, wanda a ke tsammanin shima a ranar 30 ga watan Maris zai fice daga PDP zuwa jam’iyar NNPP, inda da ga nan zai tsaya takarar shugaban ?asa.
