Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa sama da mutum 60 wa?anda aka sace daga cocin Emmanuel Baptist Church, da ke Kakau Daji sun koma ga iyalansu.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ne ya tabbatar wa BBC da hakan inda ya ce har da wasu mutane da aka yi garkuwa da su a hanyar Kachia zuwa Kaduna na daga cikin wa?anda suka samu ?ancinsu.
Ya bayyana cewa tun da farko sojoji ne suka tuntu?i gwamnatin jihar Kaduna kan cewa akwai wasu mutane da dama wa?anda aka yi garkuwa da su da ke hannunsu, inda daga baya gwamnatin Kaduna ta kar?e su kuma ta mi?a su ga iyalansu da kuma shugabannin cocin.
Kwamishinan ya ce ba shi da tabbacin ko an biya ku?in fansa kafin kar?o su ko kuma ?wato su aka yi da ?arfi.
Mambobin cocin dai sun shafe sama da wata guda a hannun masu garkuwa da mutane.
