Rahotanni daga Jihar Kaduna sun bayyana cewar gungun wasu ‘yan Bindiga ?auke da makamai sun sace ayarin wasu ‘yan sanda har su 18 akan hanyar Birnin Gwari hanya mafi hatsari a fadin Jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa an nemi ‘yan sandan an rasa bayan harin da aka kai musu a hanyar Funtuwa zuwa Birnin Gwari, an ruwaito cewa ‘yan sandan na hanyarsu ta zuwa Kano daga Minna, jihar Neja ranar Juma’a.
Amma majiyoyi sun bayyana cewa Sojoji sun ceto kimanin ‘yan sanda 10 a Maganda ranar Asabar. Shugaban kungiyar cigaban Birnin Gwari (BEPU), Barista Salisu Haruna, ya tabbatar da harin a wani jawabi. Haruna ya ce yan sandan dake Dogon Dawa sun samu labarin hakan.
Sojoji sun kwato abinsu Yace, “Kungiyar cigaban Birnin Gwari (BEPU) ta ruwaito cewa har yanzu ba’a san idan jami’an yan sanda 18 da aka kaiwa hari a hanyar Birnin-Gwari Funtuwa ranar Juma’a, 15 ga watan Junairu, 2021, suke ba. “Yan sandan 18, wadanda ke kula da hanyar Birnin Gwari Funtua, sun gamu da hari ranar Juma’a. A lokacin da ake kawo wannan rahoto, bamu san adadin wadanda abin ya shafa ba.”
Ana fargabar wasu cikin ‘yan sandan sun rasa rayukansa yayinda suks bace cikin daji.” “Rahotannin sun tabbatar da cewa yan sanda biyu sun yi waya domin sanar da gida cewa an kai musu hari amma basu san inda suke ba.”
Kungiyar cigaban jama’ar Birnin Gwari na kira ga gwamnati, da ta mike tsaye domin yaki da rashin tsaro har sai an samu nasara.”
