Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Harbe Limamin Gari

Wasu ’yan bindiga sun kai hari kauyen Kawaran Rafi da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, inda suka kashe babban Limamin garin, Dan Liman Isah.

Maharan sun tarar da marigayin har inda suka harbe shi nan take bai ko shura ba kuma suka kama gabansu ba tare da dibar wata dukiya ko satar wasu mutane ba.

Ana ganin cewa kisan gillar da aka yi wa malamin bai rasa nasaba ne da da’awarsa ta bayyana tsagwaran adawa a kan yadda ’yan bindiga ke famar cin karensu babu babbaka wajen aikata ta’addanci na kashe-kashe da garkuwa da mutane a yankin.

Jihar Kaduna dai na ?aya daga cikin jihohi a yankin Arewacin Najeriya da ke fuskantar matsalar ta’addancin ‘yan Bindiga, inda a kusan kullum jama’ar jihar ke fuskantar hare-hare musanman a yankunan Birnin Gwari da kuma sashin Kudancin Jihar da uwa uba hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bakin Kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan ta bada tabbacin shawo kan matsalolin rashin tsaro da ke addabar Jihar tare da yin kiran samun goyon baya wajen jama’a.

Related posts

Leave a Comment