Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Antaya Daji Da Tsala-Tsalan ‘Yan Mata

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar a?alla mutum 18 ?an bindiga suka sace tare da kashe mutum guda a Angwar Zalla Udawa a ?aramar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani jagora a wurin da lamarin ya faru inda ya ce cikin wa?anda aka sace har da matan aure da ?an mata.

An bayyana cewa ?an bindigan sun kai harin ne da misalin 12:30 na daren Asabar wayewar garin Lahadi a garin da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

BBC ta tuntu?i mai magana da yawun ?an sanda reshen jihar Kaduna Mohammed Jalige domin jin ?arin bayani sai dai bai amsa kiranmu ba.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ?an bindiga suka addaba inda suke ci gaba da sace mutane domin kar?ar ku?in fansa da kashe su a wani lokacin.

Related posts

Leave a Comment