Kaduna: El Rufa’i Zai Rushe Kamfanonin Tsohon Gwamna Makarfi

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai, ya soke lasisin ha??in mallaka na wasu Kamfanoni 9 mallakin tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Makarfi.

An ruwaito cewa gwamna El-Rufai ya shafa wa baki ?aya kadarorin da lamarin ya shafa jan fentin da ke nuna gwamnati na shirin rushe su ba tare da wani bata lokaci ba.

Bayanai sun nuna cewa tuni gwamnatin Malam El-Rufai ta aike da wasi?ar soke lasisi da kuma janye ha??in mallaka ga shugabannin kamfanonin da lamarin ya shafa.

A wasikun da gwamnatin Kaduna ta aike wa kamfanonin 9 ?auke da sa hannun shugaban hukumar tattara bayanan filayen Kaduna (KADGIS), Mahmud Aminu, ya ce: “An umarce ni na sanar muku da cewa mai girma gwamna Malam Nasiru El-Rufai, bisa dogaro da karfin ikon da sashi na 28 (5) (a) da (b) na kundin dokokin mallakar ?asa 1978 ya ba shi, ya soke tare da janye ha??in mallakarku.”

Da yake martani kan batun yayin amsa sakon da aka tura masa ta wayar tarho, Sanata Makarfi, ya tabbatar da cewa wasi?un soke lasisin sun iso gare shi. “Akwai matsala babba, muna kokarin ha?uwa da Ustaz Yunus (SAN) domin mu garzaya Kotu ta dakatar da gwamnatin Kaduna, yanzu suka aiko mana da wasikar sokewa guda 9.”

Daga cikin kadarorin Makarfi da gwamna El-Rufai ya biyo ta kansu a yanzu sun ha?a da Feguna 5 a Magadishu, Uku a Titin Kwato da kuma guda ?aya a Doka.

Related posts

Leave a Comment